<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>293</hymn_number>
<title>Shi Wanda Zai Daure da Duk Wahalai LW293</title>
<lyrics>[V1]
 1) Shi wanda zai daure da duk wahalai,
 Bari a koyaushe ya bi Shugaba.
 Ba zai karaya ba, ko sake nufinsa,
 Alkawari ya yi, bin Yesu zai yi.

[V2]
 2) Masu son su ƃad da shi da mugun zance,
 Suna cutar kansu, shi gaba zai yi.
 Maƙiyi zai kasa, kome dabararsa,
 Zai kama hanyarsa, bin Yesu zai yi.

[V3]
 3) Tun da ka kāre mu da Ruhun ƙarfi,
 Mun sani mun doshi rai har abada.
 Kome zai shuɗe fa, ba zan ji tsoro ba,
 Koyaushe nufina, bin Yesu zan yi.</lyrics>
</song>